Karin albashi: Saraki Ya Fara Wasu Kulle-kulle Domin Karawa Sanatoci Albashi Zuwa Milyan 15 A Wata.


Kungiyar SERAP, mai fafutikar neman daidaito da yaki da cin hanci, ta ankarar da ‘yan Najeriya yunkurin shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola, na karawa Sanatoci alawus.

SERAP ta sanar da hakan ne a wata takaitacciyar sanarwa da ta fitar a shafinta na Tuwita.

Kungiyar ta bukaci Saraki ya gaggauta jingine wannan niyya tare da saka bukatar ‘yan kasa a gaba.

Sanarwar ta SERAP ta ce, “zuwa ga Bukola Saraki, niyyar ka ta karawa Sanatoci alawus zuwa N15m ya sabawa tanadin dokar albashi.”

Kungiyar ta SERAP ce ta fara fito da wannan zance kuma ya zuwa yanzu majalisar ta dattijai ba ta ce komai a kanbatun ba.

Comments 4

Your email address will not be published.

You may also like