Karin albashi : Buhari Ya Tabo Batun Biyan Fansho Da Albashi Ya Kuma Nemi Ma’aikata Su Kara Hakuri


A jiya Talata ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi aikin da kwamitin da ya nada domin duba batun karin albashi a Najeriya su kayi inda aka nemi a karawa Ma’aikatan Najeriya albashi zuwa N30, 000
Inda Buharin yayi alkawari cewa zai duba kukan Kungiyar NLC

Shugabar wannan kwamiti ta mikawa Shugaban kasa duk aikin da su kayi bayan tsawon lokaci.

Buhari ya yabawa wannan aiki inda yace Gwamnatin sa za ta cika alkawuran da aka dauka.

Ga dai abin da ya fada jawabin na sa:

Shugaba Buhari ya bayyana cewa zai aikawa Majalisa kudirin da zai sa batun karin albashin ya shiga cikin dokar kasa.

Shugaba Buhari yayi alkawarin yin wannan ba da jimawa ba.

Shugaban kasar ya kuma nuna cewa a shirye yake da ya ga an kawo sabon kudiri a Kasar na karin albashin Ma’aikata.

Shugaba Buhari a jawabin na sa ya godewa Kungiyar NLC ta kwadago da irin kokarin da su ka rika yi na tsawon lokaci inda yace zai duba koke-koken su tare da kira da su kara hakuri a Najeriya.

A jawabin Shugaban kasar, ya nemi Ma’aikata su bi a hankali ka da a rika amfani da su wajen hura wutan rikicin siyasa a Najeriya.

Shugaba Buhari ya kuma tabbatar da cewa duk da karfin tattalin arzikin Najeriya kamar yadda ake fada, jama’a da dama su na shan wahala a gidajen su domin bunkasar tattalin arzikin bai ratsa su ba.

A dalilin haka Shugaban yace har yanzu Gwamnatin sa gyara ta ke yi a Kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma nuna cewa Gwamnatin Tarayya tana kokarin biyan tarin kudin da aka bar mata bashi na fansho da kudin sallamar Ma’aikata ne a kasar tare da taimakawa Gwamnonin wajen biyan albashi.

Shugaba Buhari a karshe ya kuma yabawa kokarin da wannan kwamiti su ka yi bayan tsawon lokaci su na bata lokacin su domin yiwa kasa hidima.


Like it? Share with your friends!

3
173 shares, 3 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like