Kano na kashe biliyan ₦9.6 wajen biyan albashi a kowane wata


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kashe kudi biliyan ₦9.6 a kowane wata wajen biyan ma’aikata albashi.

Ganduke ya bayyana haka a wajen taron kaddamar da shugabannin kungiyar kwadago NLC na kananan hukumomin jahar 44 da aka gudanar a Cibiyar Bincike da Horarwa kan Harkokin Dimakwaradiya dake Gidan Mambayya a Kano.

Gwamnan ya samu wakilicin shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Auwal Muhammad Na’iya, ya bayyana cewa biyan albashin da jihar take akan lokaci na daga cikin manyan nasarorin da ya samu idan aka yi duba da yadda ake bin wasu jihohi da dama bashin albashi.

A cewarsa ” Cigaba da biyan albashi a kowanne wata wanda a baya ba a ganin haka a matsayin wata nasara amma yanzu nasara ce saboda jihohi da dama basu iya da sauke wannan nauyi mai muhimmanci.

” A jihar Kano mu muke da mafi yawan ma’aikatan gwamnati fiye da ko wace jiha a duk fadin kasarnan,da a yanzu yawansu ya kai s185,000 duk da haka mun iya sauke nauyin biyan albashi na ₦9.6 dake kanmu a kowane wata.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like