KANO DA LEGAS SUN FI KOWACCE JAHA YIN RAJISTAR KATIN ZAƁE – INEC.


A ranar litinin ɗin nan ne dai hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta miƙa kundin mai ɗauke da adadin waɗanda rajistar zaɓe a ƙasar nan. Inda ta nuna shi ga shuwagabannin jam’iyyu.

Kundin rajistar ya nuna cewa Jihar Legas da ta Kano su suka fi kowa yawan mutanen da suka yi rajistar zaɓe. inda adadin mutanen da suka yi rajistar suka kama guda miliyan shidda da rabi a jihar Legas ( 6.5), inda kuma Kano ke da Miliyan biyar da dubu ɗari huɗu (5.4). Jihohin Bayelsa da kuma Ekiti su ne mafi ƙarancin waɗanda suka yi rajistar.wato mutane 923, 181a jihar Bayelsa, Sai kuma 909,967 a Ekiti.

Kuma sannan alƙalumma sun nuna cewa, jimillar mutane Miliyan tamanin da huɗu (84) ne suka yi rajistar zaɓen. Wato fiye da adadin yawan mutanen da suka yi a waccan kakar zaɓen ta 2015. Wanda jimillar mutane milyan 68 ne suka yi rajistar zaɓen.

Idan muka duba ta ɓangaren yanki kuma, rahotan INEC ya nuna cewa, yankin arewa maso yammacin ƙasar nan su suka fi kowa yawan masu rajistar. Inda suka haɗa jimillar mutane miliyan Ashirin (20). Wato ƙiyasin kaso 24 na jimillar rajistar gabaɗaya. Wacce take bi mata kuma ita ce, kudu maso yammaci da take da masu rajista miliyan 16. Sai kuma yankin kudu maso kudu kuma sun tashi da Miliyan sha biyu (12,000,000). Sai kuma kudu maso gabaci, Miliyan 10, sai Arewa maso gabas, Miliyan 11. sai kuma Arewa ta tsakiya mutum Miliyan 13.

Idan kuma aka duba ɓangaren rukunin shekaru, matasa ne suka fi yin rajistar zaɓen. Domin sun kai adadin miliyan 51 da ɗoriya daga jimillar masu rajistar. Yayin da rukunin dattijai kuma ya kama Miliyan 42 da ‘ƴan kai. Kamar yadda premium times ta rawaito.


Like it? Share with your friends!

3
83 shares, 3 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like