Kannywood: Sulaiman Bosho Zai Fuskanci HukunciKungiyar ladabtar da jarumai maza da mata Moppan ta fitar da wata sanarwa a safiyar shekaran jiya talata cewa: zata hukunta jarumin barkwanci Sulaiman Bosho bisa laifin dori akan abinda darakta ya umarce shi wato over role kenan.

Acewar Moppan: “Mun jima muna ganin kura kuran da Bosho Yake Yi a cikin fim, mun kira shi dan ya gyara amma ya kasa gyarawa.”

“Mun tuhumi daraktocin da suke da suke sa shi a cikin fim amma sunce, su basu ga laifi ko munin kalamansa ba. 

Dan haka ne muka yanke hukuncin hukunta daraktocin da kuma shi jarumi Bosho”. Inji Moppan.

Hukuncin da za’ayi wa jarumi Bosho akwai tara wanda aka ci Bosho dan wannan ya zama izna a gare shi dama daraktocin da suke bashi umarnin furta kalaman da basu dace ba.

Da muka tambayi Bosho akan da wacce fuska ya kalli wannan hukuncin? 
Sai ya amsa da cewa:”Wannan hukunci son ransu suka aikata, domin mutane sune ya kamata su gane laifin da muka aikata ba su ba, domin mutane sune masu kallon mu, sune alkalai ba Moppan ba.”

Comments 0

Your email address will not be published.

Kannywood: Sulaiman Bosho Zai Fuskanci Hukunci

log in

reset password

Back to
log in