(Kannywood): Adam A Zango Ya Nemi Gafarar Ali Nuhu


Shahararren jarumin fina-finan Hausa na Kannywood, Adam A Zango, ya nemi gafarar jarumi Ali Nuhu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Sakon mai dauke da wani hoton da ya nuna Zango ya durkusa kuma Ali na zaune bisa kujera, ya zo ne kwanaki bayan Zangon ya wallafa wasu hotunansa da Ali a Instagram bayan sun kwashe kwanaki suna “gaba”.

Sakon Adam Zangon ya ce “tuba nake sarki gwiwowina a kasa”.

Tuni dai magoya bayan jarumin suka fara tofa albarkacin bakinsu kan hoton da Zangon ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Jaruman biyu suna gaba-gaba a masana’antar Kannywood din inda suke da mabiya da dama a shafukan sada zumunta.


Like it? Share with your friends!

-1
77 shares, -1 points

Comments 6

Your email address will not be published.

  1. Wallahi wan nan shi yafi masu a matsayinsu na jigo a harkan kannywood, domin gaba bashi da wani amfani ko a musulunce ne, su kuma munafukan da suke shiga tsakaninsu sai suji kunya. Shi kuma SARKI ALI NUHU DA WAZIRIN NASA WATO ADAM ABDULLAHI ZANGO ADDU’A NAKE MASU ALLAH ya kara masu kwarin gwiwa da fasaha gami da jajircewa wajen tafiyar da harkokinsu da sukasa gaba.

  2. Amma gaskiya damamaki acekama yanda sarki ali nuhu da xango susamu matsala amma inamamatukar baiwa zango shawara gaskiya sunada makiya gaskiya zango yabarbarin anajinkansu shawaratakenan nabarku lafiya

You may also like