Kanin Aisha Buhari ya tsaya takarar gwamnan Adamawa


Mahmud Halilu Ahmad, kanin matar shugaban kasa, Aisha Muhammad Buhari ya shiga takarar gwamnan jihar Adamawa.

Hoton Halilu rike da fom din takara tare da shugaban kasa, Muhammad Buhari ya jefa shakku a zukatan wasu yan jam’iyar.

“Kamata ya yi shugaban kasa, ya zama uba ga kowa.kamata ya yi ya dauki hoto da dukkanin yan takara,” a cewar wani dan jam’iyar da ya nemi a boye sunansa.

A wajen kaddamar da takararsa a Yola, a jiya Litinin, Mahmud wanda akafi sani da Modi ya zargi gwamna Bindow da rashin gaskiya da kuma yin watsi da dukkan bangarori.

Halilu ya yi alkawarin matukar aka zabe shi to zai yi aiki da shugabannin jam’iyar wajen gyara rashin adalcin da ake yi a jihar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like