
Kamfanin sadarawa na MTN ya bada gudummawar kuɗi dalar Amurka miliyan $25 ga kungiyar Tarayyar Afrika AU domin taimakawa shirin kungiyar na sayan allurar riga-kafin cutar Korona .
Kamfanin yace gudunmawar za ta taimaka a samu damar sayen allurar riga-kafin har kusan miliyan 7 da za a yiwa ma’aikatan lafiya dake nahiyar wanda hakan zai taimakawa shirin riga-kafi na hukumar dake dakile yaduwar cututtuka a nahiyar Afrika ACDC.
Shugaban kamfanin na MTN, Ralph Mupita ya ce barnar da cutar ta Covid-19 ta yi ya nuna cewa akwai bukatar gwamnatoci da kuma kamfanoni masu zaman kansu su hada kansu idan ana so shawo kan annobar.
Da yake magana kan batun shugaban hukumar ta A-CDC ,John Nkengason ya ce burinsu shi ne a tabbatar da cewa dukkanin mutanen da suke buƙatar a yi musu riga-kafin an yi musu.
Comments 23