Kamata ya yi dan kudu ya maye gurbin Buhari – Kabiru Gaya


Sanata mai wakiltar mazabar kudancin Kano a majalisar dattawa, Kabiru Ibrahim Gaya ya ce yankin kudancin Najeriya ne ya kamata ya samar da shugaban kasa.

Da yake jawabi a wurin taron da kamfanin kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya shirya ranar Talata a Abuja,Gaya ya ce shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya fito daga yankin arewa yana kokari wajen gina kasarnan.

Ya ce ya yarda cewa shugaban kasar da zai hau anan gaba ya fito daga kudancin kasarnan.

“Kan batun shugaban kasa a 2023. Zan goyi bayan shugaban kasa daga yankin kudancin kasarnan. Ina ganin lokaci yayi da zamu samu shugaban kasa daga ɓangaren kudancin kasarnan yayin da mataimaki zai fito daga arewa,” ya fada.

Ya kara da cewa hakan ne zai sa kowane yanki yaji ana damawa da shi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like