An kama mutane 5 dake da hannu a hari kan ɗalibai ƴan Najeriya a India


Master

ƴan sanda a ƙasar India sun tsare mutane biyar kan zarginsu da hannu wajen kai hari akan dalibai yan Najeriya, a garin Greater Noida dake arewacin kasar.

A kalla yan Najeriya hudu ne suka samu raunuka a harin, hare-hare kan yan ƙasashen Afirka birnin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi dan shekaru 15 da ake zargin wasu yan Najeriya da bashi miyagun ƙwayoyi.

Ranar talata Ƙungiyar ɗalibai ƴan Afirka da suke karatu a India ta shawarci dalibai yan Afirka mazauna birnin da su kasance a cikin gidajensu.

Ƴan uwan ɗalibin da yarasu sun shigar da ƙara inda suke zargin dalibai ƴan Najeriya da bawa matashin miyagun ƙwayoyi, bayan mutanen unguwar sun sanar dasu cewa, yaron na zama da wasu dalibai ƴan Najeriya.

Tun farko a ranar litinin jami’an tsaro sun kama wasu ɗalibai ƴan Najeriya su biyar suka ƙwace fasfunansu, sai dai sun sake su daga bisani saboda rashin ƙwararan shedu. Hakan dai bai yiwa iyalin dalibin ɗadi ba

Da yammacin ranar dubban mutane masu zanga-zanga sun kewaye ofishin ƴansanda da kuma kotun dake yankin.

A wani abu dake nuna ramuwar gayya, masu zanga zangar sun lakaɗawa wasu ƴan Najeriya duka inda suka barsu kwance a titi cikin jini.

 

 

 


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like