Kaduna:An kashe mutane 20 a wani sabon hari da yan bindiga suka kai


Akalla mutane 20 aka kashe a wani sabon hari da ake zargin fulani makiyaya da kaiwa kan kauyen Anguwan Aku a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Wasu da dama ne kuma suka jikkata a harin.

A cewar wani mazaunin kauyen harin ya faru ne da misalin ƙarfe bakwai na safiyar ranar Litinin.

Ya ce maharan na sanye ne da kayan sojoji dauke da bindigogi kirar Ak-47, adduna da kuma sanda.

“Suna harbin kan me uwa da wabi mutane suka fara gudu cikin daji. Sun rika binmu yayin da muke gudu cikin daji an kashe wasu daga cikin mu a cikin daji.”

“Wasu daga cikinsu na sanye da kakakin sojoji da kuma rigar sulke na gansu daga wurin da nake boye.”

Mutumin ya kara da cewa akwai rade-radin yiyuwar kawo harin kuma gwamnan jihar na sane da haka amma bata dauki wani mataki ba.


Like it? Share with your friends!

1
85 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like