Juyin mulki: Gudluck Jonathan ya koma kasar Mali


A kokarin da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ke yi kan sansanta rikicin siyasar kasar Mali, manzo na musamman da kungiyar ta nada kan sasanta rikicin, wato tsohon shugaban kasar Najeriya, Gudluck Jonathan ya isa Bamako babban birnin kasar.

Tsohon shugaban kasar shi ne ya sanar da haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Gudluck ya ce sun koma Bamako ne domin cigaba da tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a kokarin da ake na dawo da kasar kan mulkin farar hula.

Rikicin siyasa ya barke ne a kasar tun bayan da sojoji suka hanbarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 22

Your email address will not be published.

You may also like