Jonathan ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa kasar Mali


Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar Mali domin sulhunta rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar.

Idan za a iya tunawa kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS ve ta nada Jonathan a matsayin manzo na musamman kan rikicin siyasar kasar Mali.

A makon da ya gabata ne sojoji suka hanbarar da gwamnatin shugaba,Aboubakar Keita biyo bayan zanga-zangar adawa da yan kasar suka jima suna yi.

Ana ran tawagar zata mayar da hankali wajen tursasa dakarun da suka yi juyin mulkin su sako tsohon shugaban ƙasar daga inda yake tsare.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 27

Your email address will not be published.

You may also like