Jonah Jang ya yi Atiku alkawarin kuri’u miliyan 2


Toshon gwamnan jihar Plataeu,Jonah Jang ya ci alwashin goyon bayan, Atiku Abubakar dantakarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyar PDP tare da sama masa akalla ƙuri’u miliyan biyu daga jihar domin tabbatar da nasararsa a zabe mai zuwa.

Jang ya bayyana haka ranar Litinin lokacin da yakewa magoya bayan jam’iyar jawabi a wurin taron gangamin yakin neman zabe a Jos babban birnin jihar.

Ya ce: ” Plataeu ta PDP ce haka ma PDP ta jihar Plataeu ce.Za mu tabbatar da cewa mun bawa, Alhaji Atiku Abubakar dantakarar shugaban kasa na jam’iyar kuri’u miliyan biyu a zaben dake tafe.”

Tsohon gwamnan ya zargi gwamnatin tarayya ta jam’iyar APC da jawowa kasarnan koma baya ta hanyar kawo wasu tsare-tsare da manufofi marasa inganci.

Ya yin da yake bayyana amincewarsa cewa PDP zata lashe zaben shugaban kasa, ya shawarci Jam’iyar APC da su shirya amincewa da sakamakon faduwa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like