Jirgin sojan saman Najeriya ya fado a yankin arewa maso gabas


Rundunar sojan sama ta Najeriya ta ce wani jirginta mai saukar ungulu ya rikito kasa yayin yaki da masu tayar da kayar baya a arewa maso gabashin kasar.
Sanarwar da mai magana da yawun sojin kasar Ibikunle Daramola ya fitar, ta ce daman jirgin mai saukar ungulu ya na taimakawa dakarun sojin kasa ne da ke yaki da ‘yan Boko Haram lokacin da abin ya faru a garin Damasak da ke jihar Borno da maraicen jiya Laraba.
Sai dai sanarwar bata bayyana musabbabin faduwar jirgin ba, da kuma mutanen da ke cikinsa lokcin da ya yi hatsrin da ko an yi asarar rayuka ko jikkata.
A baya-bayan nan sojojin Najeriya sun zafafa kai hare-hare maboyar ‘yan Boko Haram, a yankin na arewa maso gabashin kasar.
Hakan na faruwa ne a didai lokacin da su ma ‘yan Boko Haram, da mayakan da sukai mubaya’a ga kungiyar IS suke ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin.
Ana ci gaba da nuna fargaba kan yadda rashin tsaro ya sake kunnukai a jihar Borno da kewaye a daidai lokacin da Najeriya ke tunkarar babban zaben da ake sa ran za a yi a wtan Fabrairu mai zuwa.


Like it? Share with your friends!

1
80 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like