Jirgin kasa ya kashe wasu mutane biyu a Kano


Ƴansanda a jihar Kano a ranar Talata sun tabbatar da mutuwar mutane biyu wadanda jirgin kasa ya markade su har lahira.

DSP Abdullahi Haruna mai magana da yawun rundunar yansandan jihar shine ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar.

Haruna ya ce “Ranar 16 ga watan Afirilu da misalin karfe 8 na safe mun samu rahoton cewa wasu mutane da ba a gane ko suwaye ba dake kwance akan digar jirgi kasa, jirgin ya talutse su har lahira a bayan Kano Club dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar.”

A cewarsa lokacin da yansanda suka isa wurin da lamarin ya faru sun gano cewa daya daga cikin mamatan jirgin ya datsa shi gida biyu.

Mai magana da yawun rundunar ya yi kira ga jama’a da su kaucewa digar jirgi domin gudun faruwar hatsari makamancin wannan.


Like it? Share with your friends!

4
62 shares, 4 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like