Jikan Sheik Nyass Zai Raba Raguna Guda 2500 Ga Mabukata


Babban limamin masallacin Maulanmu Shehu Ibrahim Inyass RA, Maulana Sheikh Tijjani Cisse RTA ya sayo raguna 2500 wadanda zai rabawa marasa karfi wadanda basu da ikon sayan abin layya a garin Kaulaha. Sheikh Tijjani Cisse na daya daga cikin mutane 50 cikin musulmai 500 wadanda suka fi kowa tasiri da karfin fada aji a duniyar musulunci.

Idan ba’a manta ba a ranar 31 ga watan da ta fita dan uwansa Sheikh Mahi Cisse shima ya raba ragunar layya guda 150 ga talakawa, sannan ance kamin salla zai kara raba wadansu daruruwan ragunar.

Irin wannan aikin alhairin ba yau iyalan Shehu suka fara ba, kowa ya shaida duk yawan jama’an da suke zuwa maulidi kowa sai yaci liyafa ya ture. Allah ya saka musu da alhairi amin.

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like