Jihar Zamfara Ce Ta Fi Yawan Matalauta A NajeriyaRahoton wanda ya biyo bayan wani bincike da hukumar ta gudanar a duk fadin Najeriya, ya bayyana cewa jihar Zamfara ce ke kan gaba da mutane da ke fama da fatara, inda take da matalauta 3,836,484 a cikin iyalai 825,337.

A cewar rahoton, jihar Kebbi da ke makwabtaka da jihar ta Zamfara ma tana gaba-gaba a yawan jama’a masu fama da talauci, inda ta ke da 3,745,427 da aka samu a cikin iyalai 807,261, yayin da jihar Kano take da matalauta 2,697,160 a cikin iyalai 542,764.

Jihar Borno na da karancin masu fama da fatara a cewar rahoton, inda ta ke da matalauta 157,841 a cikin iyalai 30,957, ita kuwa jihar Ondo tana da 171,119 a cikin iyalai 48,518.

Jihar Ekiti ce ke da mafi karancin mutane da ke da talauci 94,923 daga cikin iyalai 32,949.

Rahoton ya bayyana cewa babban birnin tarayya Abuja na da matalauta 511,353 a cikin iyalai 141,776, yayin da jihar Legas ta ke da 1,848,767 daga cikin iyalai 466,120.

Shugaban sashen watsa labari na hukumar kula da wadatar al’umma ta NASSCO da ke karkashin ma’aikatar jin kan jama’a ta Najeriya, Joe Abuku wanda ya ba da rahoton binciken ga ‘yan jarida, ya ce an kafa hukumar ne a shekarar 2016, a karkashin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da Bankin Duniya.

Ya ce ita kuwa hukumar binciken ta NSR an kafa ta a zaman wani sashe na aikin NASSCO, tare da manufar samar da sahihan bayanai da kididdiga na masu fama da fatara da talauci a Najeriya.

Masu fashin baki dai na ta’allaka yanayin talauci da fatara a jihar Zamfara, musamman da yanayin kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta tsawon shekaru, wanda ya gurgunta tattalin arzikin jihar.

Wan sansanin 'yan bindiga da dakarun Najeriya suka tarwatsa a jihar Zamfara (Hoto- Shafin twitter na sojojin Najeriya)

Wan sansanin ‘yan bindiga da dakarun Najeriya suka tarwatsa a jihar Zamfara (Hoto- Shafin twitter na sojojin Najeriya)

Manazarta kuma sun dade suna bayyana irin yadda ayukan ‘yan bindiga a jihar, da suka hada da kai hare-hare kan garuruwa da kasuwanni, da kisan jama’a da satar mutane domin karbar kudin fansa, suka gurgunta ayukan noma da kiwo da ma sha’anin kasuwanci a tsakanin al’ummar jihar.


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg