Jean Claude Van Damme Ya Koka Bisa Daina Sa Shi A Fina-Finai Da Akayi Tun Bayan Musuluntar Sa


Shahararren jarumin fina finan turanci na kasar America Jean Claude wanda akafi sani da suna Van Damme, ya karbi addinin musulunci.

Jarumin ya bayanna cewa yana fuskanci kalubale da dama bayan karbar addinin musulunci da yayi,inda daraktoci da manyan masu ruwa da tsakaki suka daina bashi aiki da sanya shi acikin fina finan su

A Rahoton da Bbc ta samu Van Damme ya kara da cewa yayi karatu mai zurfi na kiristanci wanda hakan shi ya bashi damar gane cewa addinin musulunci shine addinin na gaskiya a duniya,kuma shine addinin mafi tsafta da zaman lafiya.

Van Damme ya cigaba da cewa duk da yawan tsangwama da gori da ‘yan uwansa da abokan aikinsa suke masa hakan baisa zuciyar sa ta karaya ba,saboda yasan cewa yana akan hanya madaidaiciya sannan yayi riko da Allah da manzonsa Annabi Muhammad (S.A.W),kuma yana da yakinin bazai taba yin danasani ba.

A karshe Jean Claude Van Damme yayi kyakkyawar addu’a ga sauran abokansa dake akan addinin kiristan kuma yana masu kwadayin shigowa addinin musulunci domin su samu rahamar Allah don samun kyakkyawar gobe.

Comments 4

Your email address will not be published.

  1. MY LOVELY SUPER STAR. VAN DAMME. I LOVE YOU. DONT TO WARRY ALLAH IS WITH YOU EVERY WHERE YOU ARE. ALLAH WILL BLESS YOU.

You may also like