Jamus ta kasance daya daga cikin kasashen da ta yi cinikin wadannan kayan ma su daraja da kuma dimbin tarihi, daga hannun wasu kasashen Turai da suka karbe kayan daga Afirka, kuma tuni ta dauki matakin shirya yadda za a mayar da kayayyakin asalinsu na farko. Ministan harkokin wajen Jamus, Heiko Maas, ya ce, cimma matsaya na mayar ma Najeriya kayayyakin ta, wani sabon babi ne na shawo kan kuskuren tarihi na mulkin mallaka. Gumakan na Benin, suna tattare da tarihi irin na mulkin danniya da aka yi ma jama’a a wancan lokacin. An shirya mayar da wadannan kayayyakin Najeriya a shekarar 2022 mai zuwa kamar yadda gwamnatin Jamus din ta sanar.

Jamus ta amince a yi abin da ta ce, shi ne adalci, an wawushe wadannan kayan daga akasarin kasashen da aka yi ma mulkin mallaka Afrika a karni na sha tara, kayan al’adun gargajiyar da aka fi sani da Benin Bronzes, an sayar da su ga kasashen Turai da suka nuna sha’awarsu. Dakin adana kayan tarihin Jamus na birnin Berlin yana dauke da wadannan kayan kimanin 530 na masarautar Benin da ke yankin kudancin Najeriya. An kiyasta cewa, an yi awon gaba da wadannan kayayyakin a shekarar 1897.