Mako daya bayan mummunan ibtila’in ambaliyar da ya shafi yammaci da arewacin Jamus, gwamnatin kasar ta ware euro miliyan 200 daga baitul malinta dan tallafawa wadanda matsalar ambaliyar ta shafa.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da su kuma hukumomin yankunan da matsalar ta fi kamari, za su samar da tallafin gaggawa na euro miliyan 400 ga jama’a, a matsayin agajin sake inganta gidaje da hanyoyin da suka ruguje a jihohin biyu, daya ta Arewa da ta yammacin Jamus.