Hukuncin kotun na wannan Jumma’a ya ce a tsakanin watan Afrilu na shekarar 2019 zuwa watan Nuwambar bara, mutumin mai shekaru 32 ya sanya rayukan mutane cikin hatsari a wani karamin gari da ake kira Gundelsheim da ke jihar Baden-Wuerttemberg a kudu maso yammacin Jamus.
Duk da cewa gobarar da ma’aikacin kashe gobarar ya haddasa ba su ci rayukan jama’a ba amma kotu ta ce barnar da mutumin ya haddasa ta kai ga lalata kadarorin da darajarsu ta kai Euro 500,000. Bajamushen dai ya amsa laifunsa ya kuma alakanta abin da ya aikata da cutar damuwa da yake fama da ita.