Wani jirgin saman sojin Jamus dauke da ma’aikatan lafiya da kuma kayyayakin kiwon lafiya ya sauka birnin Delhi. Indiya na zama kasar da annobar Corona ta ke yi wa mummunar barna a yan makwannin nan.

Baya ga kwararru kan kiwon lafiyar da Jumus ta aike wa kasar ta Indiya, akwai na’urorin shakar numfashi na Ventilator guda 120.

Ta’azarar cutar a kasar ta Indiya ya jefa kasashe makwabata cikin tararrabi da suka hada da Nepal da Pakistan da kuma Bangladash.