Kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa ya ruwaito cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ta afku a Jamus ta haddasa asarar sama da dalar Amirka biliyan biyu. Rahotanni sun nunar a cewa wata majiyar gwamnati ce ta tabbatar da hakan,biyo bayan ambaliyar da ta afku a yammacin kasar a makon da ya gabata.

Ma’aikatar sufurin kasar ta bayyana cewa, kiyasin barnan da ambaliyar ta yi sun hadar da layin dogo na jiragen kasa wadanda aka ce zai lakume sama da biliyan daya na dalar Amirkan, yayin da sauran gadoji da hanyoyin mota gami da turakun intanet za su ci kusan biliyan guda, kuma za a fara aikin gyaran su cikin gaggawa.

Tattaunawa ta yi nisa tsakanin bangarorin gwamnati da masu ayyukan. Wannan dai shi ne karo na farko da Jamus ke fuskantar iftila’i irin wannan. Lamarin da ya sa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel yin kira domin daukar matakan gaggawa a kan yaki da sauyin yanayi.