Ana ganin cewa wannan gangamin rigakafin ya kara yawan wadanda suka sami allurar a nahiyar Turai a cewar Jens Spahn da ke zama ministan lafiya a Jamus.

Ya ce wannan mataki ya nuna irin hanzarin da za su iya cimma wa a cikin kankanin lokaci. Baya ga kasashen China da Amirka da Indiya babu wata kasa da ta yi yawan allurar da Jamus din ta yi a ranar Laraba ba.

Birtaniya ta kwatanta inda a cikin sa’o’i 24 ta yi wa sama da mutum dubu dari takwas rigakafin.

Yanzu dai sama da kashi 25 cikin 100 na al’umma a Jamus sun karbi kason farko na rigakafin yayin da dama daga cikinsu sun kammala duka.