Jam‘iyyar adawa ta PDP, ta yi alkawarin zata ciyar da ‘yan Najeriya har sai sun koshi, saboda a cewarta ba zata lamunci yunwar da gwamnatin jam’iyyar APC a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kakaba ma yan Najeriya ba.

Shugaban jam’iyyar, Uche Secondus ne ya bayyana haka a yayin gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da aka gudanar a garin Dutse, babban birnin jahar Jigawa.

Majiyarmu ta ruwaito Secondus yana kira ga jama’ar jahar Jigawa dasu tabbata sun zabi Atiku a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a ranar 16 ga watan Feburairu, matukar suna son ganin sun rabu da talauci, yunwa da fatara.

Bugu da kari, Secondus yace idan aka duba cincirindon jama’ar da suka halarci gangamin yakin neman zaben Atiku a garin Dutse, da ma wadanda suka halarci tarukan da suka yi a jihohi daban daban, ta tabbata PDP ce zata lashe zaben 2019.Haka zalika shugaban na PDP ya tabbatar ma jama’an jihar Jigawa cewa Atiku Abubakar yana da kwarewa da kuma gogewar data dace da mulkin Najeriya, don haka ba zai basu kunya ba idan har suka bashi goyon baya ya zama shugaban kasa.

Daga karshe Secondus ya jaddada ma jama’an jahar Jigawa cewa Atiku Abubakar dansu ne, saboda mahafiyarsa data rasu yar asalin garin Dutse ce, don su rike shi tamkar dansu da muhimmanci, saboda a cewarsa Buhari bai cika alkawurran daya daukar musu ba.

Shima a nasa jawabin, tsohon gwamnan jahar Jigawa, Sule Lamido yayi kira ga jama’a dasu zabi Atiku Abubakar a yayin zaben shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Feburairu, saboda a cewarsa Buhari ya gaza ta kowanne fanni.