Jam’iyyar PDP Ta Maida Martani Ga Shugaba Buhari


Jam’iyyar PDP ta mayarwa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari martani kan wasu kalamai da aka rawaito shugaban ya yi, na cewa gwamnatinsa ta fi ta tsohon ssugaban ƙasar Goodluck Jonathan taɓuka abin kirki.

”Ka gaza” a cewar PDP, kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a ta bakin kakakinta Kolawole Olagbondiyan.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa abubuwa da dama sun dagule a zamanin gwamnati mai ci daga shekaru biyar na hawanta zuwa yanzu.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa ”Ba mamaki rayuwar jin dadi da annushuwa da shugaban yake yi a fadarsa ta Asovilla ce ta sanya shi bugun ƙirjin cewa al’amura na tafiya dai dai a gari.

”Ya kamata shugaba Buhari ya san da sanin cewa a yayin da yake jin daɗinsa a fadar shugaban ƙasa, ƴan Najeriya da dama na kwana da yunwa, fiye da mutum miliyan 30 sun rasa harkokin kasuwancinsu miliyoyi kuma basa iya tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum saboda ƙangin rayuwar da ta jefa su a ciki” in ji PDP.


Like it? Share with your friends!

-2

Comments 101

You may also like