Jam’iyun siyasa 56 sun shirya fafatawa a zaben 2019-INEC


Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta ce jam’iyun siyasa 56 cikin 91 da aka yiwa rijista a kasarnan sun shirya shiga zaben shekarar 2019.

Obo Effanga, kwamishinan zaben jihar Rivers shine ya bayyana haka ranar Juma’a lokacin da yake ganawa da yan jaridu a Fatakwal.

Ya ce INEC na sha’awar shigar dukkanin jam’iyyun 91 inda ya kara da cewa hukumar za ta yi hulda ne kawai da jam’iyun siyasar da suka yi rijistar shiga zaben.

Kwamishinan zaben ya tabbatarwa da mutanen jihar Rivers cewa hukumar ta shirya gudanar da zabe mai cike da gaskiya da adalci ya kara da cewa za a tabbatar an tanadi dukkanin kayayyakin da ake bukata gabanin ranar zaben.

Effanga ya ce duk wani mai kada kuri’a da ba a tantance da na’urar Card Reader ba to ba zai samu damar kada kuri’a ba.


Like it? Share with your friends!

1
88 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like