Jam’iyun PDP da APC sun yi ruwan kuɗi a zaɓen jihar Ekiti


Yanzu dai za a iya cewa tafaru takare wai anyi wa mai dami ɗaya sata, zaben gwamnan jihar Ekiti ya kammala lafiya kuma tuni aka bayyana Kayode Fayemi a matsayin mutumin da ya samu nasara a zaɓen.

Sai dai zaɓen ya nuna yadda har yanzu kuɗi ke yin tasiri wajen sauya ra’ayin masu kada kuri’a.

Dukkanin jam’iyyu biyu dake kan gaba a zaben wato APC da PDP sun yi amfani da kudi wajen shawo kan masu kada kuri’a su zaɓe su.

Bincike da Jaridar Premium Times da kuma The Cable suka gudanar ya nuna yadda wakilan jam’iyun biyu suka rika sayen kauria kan kudin bada bai gaza ₦3000.

Ya yin da jam’iyar APC ta rika rabon naira ₦5000 kan kowacce kuri’a Ita kuwa jam’iyar PDP mai mulkin jihar kuma ta rika raba ₦3000.

Duk da cewa dokar zaɓe ta kasa ta haramta yin haka kuma duk mutumin da aka samu da bayarwa ko kuma karba to za a yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni 12 ko kuma zabin tarar kuɗi ₦500,000 ko kuma alkali ya hada duka gaba daya.

Sai dai duk da cewa hakan na faruwa ne a idon jami’an tsaro, jami’an tsaron sun nuna rashin damuwa kan abinda ya faru.

Abin jira a gani shine ko yaushe ne siyasar Najeriya za ta bunkasa ta yadda mutane za su san yancinsu a matsayin su na yan kasa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like