Jam’iyar PDP ta nemi a soke kuri’u 515,951 na zaben gwamnan Kaduna


Jam’iyar PDP da kuma Isa Ashiru dantakarta na gwamna a jihar Kaduna, a ranar Litinin za su yi kira ga kotun sauraron karar zaben gwamna jihar Kaduna da ta soke kuri’u 515,951 da tace an kara sune ba bisa ka’ida kan kuri’un da aka kada a zaben gwamnan jihar.

Kotun ta tsayar da ranar 19 ga watan Agusta a matsayin ranar da zata karbi bayanai na karshe a rubuce daga lauyoyin yan takarar biyu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya samu yin tozali da rubutaccen bayanin da jam’iyar PDP zata gabatarwa kotun.

Cikin kunshin bayanin jam’iyar PDP ta nemi kotun ta ayyana Ashiru a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar ta yin la’akari da halastattun kuri’un da aka kada.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like