Jam’iyar APC ta sake rasa mambobi huɗu a majalisar wakilai


Mambobin majalisar wakilai hudu da suka fito daga jam’iyar APC sun sanar da fitarsu daga jam’iyar.

Mambobin hudu sun hada da Lam Adesina da Dada Awoleye daga jihar Oyo, Segun Williams daga jihar Ogun da kuma Lawali Hassan daga jihar Zamfara.

Yakubu Dogara, Kakakin majalisar wakilai ta tarayya shine ya sanar da sauya shekar wakilan a zaman majalisar na ranar Talata.

Yan majalisun hudu sun koma jam’iyu daban-daban.

Awoleye ya koma jam’iyar Accord, William ya koma jam’iyyar Labour ya yin da Adesina ya koma jam’iyar ADC.

Shi kuwa Lawali Hassan dake wakiltar mazabar Anka/Mafara ya koma ne jam’iyar PDP.


Like it? Share with your friends!

2
101 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like