Jam’iyar APC ta nesanta kanta da abin da yafaru a majalisar tarayya


Jam’iyar APC mai mulki tayi allawadai da mamaye harabar majalisar tarayya da wasu jami’an tsaron DSS suka yi.

Jam’iyar cikin wata sanarwa da, Yekini Nabena mai rikon mukamin kakakinta na kasa ya fitar, ta nisanta kanta daga abin da yafaru.

Jam’iyar ta jaddada biyayyarta ga bin doka da oda inda ta shawarci bangarorin gwamnati da su cigaba da bin tanada-tananden kundin tsarin mulkin kasa.

Ta kuma yi kira da a kara samun alakar gudanar da aiki mai kyau tsakanin dukkanin bangarorin daban-daban.

Sai dai jama’a da dama na ganin cewa sanarwar da jam’iyar ta fitar tamkar borin kunya ne biyo bayan sanarwar da ta fitar tunda fari kan killace harabar majalisar kasa da jami’an tsaron DSS suka yi.


Like it? Share with your friends!

1
103 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like