Jam’iyar APC ta lashe kujerar sanata mai wakiltar mazabar Taraba ta tsakiyaSanata Yusuf Abubakar Yusuf dake wakiltar mazabar Taraba ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC ya sake cin zabe biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa dana yan majalisun kasa da aka gudanar ranar Asabar.

Hukumar zabe ta INEC ce ta bayyana haka ta bakin jami’in tattara sakamakon zaben kujerar sanata mai wakiltar mazabar.

Jami’in ya sanar da sakamakon ne a a garin Bali dake da tazarar kilomita 230 daga Jalingo babban birnin jihar.

Abubakar ya samu kuri’u 98,860 inda ya kayar da babban abokin takararsa,Dahiru Bako na jam’iyar PDP wanda ya samu kuri’u 93,074.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like