Jam’iyar APC ta kara rasa wakilai biyu a majalisar wakilai ta tarayya


Jam’iyar APC a majalisar wakilai ta kara rasa mambobinta biyu inda suka koma jam’iyun adawa.

Yan majalisun biyu da suka fice daga jam’iyar ta APC a ranar Alhamis sun hada da Stephen Olemija daga jihar Ondo da kuma Ahmed Abu daga jihar Niger.

Olemija ya koma jam’iyyar AA yayin da Abu ya koma Jam’iyyar SDP.

Sun bayyana dalilansu na barin Jam’iyar ta APC cikin wasikar da kowannensu ya aikewa zauren majalisar wacce kakakinta, Yakubu Dogara ya karanta.

Yan majalisun sun dora alhakin barinsu jam’iyar kan rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani.

Zaben fidda gwanin yan takarkaru da jam’iyar APC ta gudanar cike yake da rikici.

Sauya shekar wakilan biyu na zuwa ne kwana ɗaya bayan da wasu wakilai biyu yayan jam’iyar ta APC suka sauya sheka.


Like it? Share with your friends!

1
86 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like