Jam’iyar APC ta tabbatarwa da Shehu Sani tikitin takara


Uwar jam’iyar APC ta kasa ta dage kan matsayinta na cewa, Shehu Sani shine halattaccen dantakararta na kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya.

Yekini Nabena, mai rikon mukamin kakakin jam’iyar shine ya bayyana haka ga kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce ,Sani shine dantakara daya tilo daga shiyar da uwar jam’iyar ta kasa ta amince da shi inda ya dage cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa’i bai isa ya fadawa jam’iyar abin da ya kamata ta yi ba.

El-Rufai ya ki amincewa da tikitin kai tsaye da jam’iyar ta bawa sanata Shehu Sani inda ya ce daya daga cikin masu taimaka masa, Mallam Uba Sani ya cancanci tsayawa takara.

Reshen jihar na jam’iyar ya gudanar da zaben fidda gwani inda aShehu Sani ya yi rashin nasara a hannun Uba Sani.

A cewar Nabena zabe ya gudana a shiyar na yan majalisar wakilan tarayya da kuma na majalisar dokokin jihohi amma a kujerar sanata Shehu Sani muka sani dan takara.


Like it? Share with your friends!

-1
76 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like