Jam’iyar APC ta dakatar da mataimakin gwamna Yahaya Bello


Jam’iyar APC reshen jihar Kogi ta dakatar da mataimakin gwamnan jihar Simon Achuba.

Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da majalisar dokokin jihar ta kaddamar da fara shirin tsige Achuba wanda ya dade yana takun saka da gwamnan jihar,Yahaya Bello.

Achuba ya yin zargin cewa gwamnan jihar ya hana a biya shi albashinsa da kuma wasu alawus da suka kama miliyan 800 sakamakon umarnin da gwamnan ya yi.

Ya kuma kara da cewa gwamnan na neman ya kashe shi.

Abdullahi Bello, shugaban jam’iyar APC na jihar ya fadawa manema labarai ranar Alhamis cewa an dakatar da mataimakin gwamnan kan zagon kasa da ya yiwa jam’iyar gabani da kuma bayan zaben shekarar 2019.

Ya kara da cewa kwamitin da aka kafa ya binciki Achuba ya same shi da aikata laifi inda ya bayar da shawarar dakatar da shi.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like