Jam’iyar APC ta dakatar da Amosun, Okorocha


Shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya dakatar da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosu da kuma Rochas Okorocha na jihar Imo.

Har ila yau shugabancin jam’iyar ya bawa kwamitin zartarwar ta shawarar korar su daga jam’iyar baki daya.

Shugabancin jam’iyyar ya cimma wannan matsaya ne a wani taro da ya gudanar ranar juma’a a Abuja inda aka zargi mutanen biyu da laifin yin zagon kasa ga jam’iyar.

Dukkanin mutanen biyu sun lashe zaben kujerar sanata karkashin jam’iyar a zaben da ya gabata na ranar Asabar.

Sun raba gari ne da shugabancin jam’iyyar APC na kasa bayan da yan takarar da su ke goyon baya su gaje su suka gaza samun tikitin takara a jam’iyarts ta APC.

Yayin da Okorocha ke goyon bayan surukinsa, Uche Nwosu a matsayin mutumin da zai gaje shi a daya bangaren Amosu na goyon bayan Adekunle Akinlade wanda wakili ne a majalisar wakilai ta tarayya.

Akinlade na takara a jam’iyar APM ya yin da Nwosu ke takara a jam’iyar AA.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like