Jam’iyar APC a jihar Rivers ta nemi a dage zaɓuka a jihar


Jam’iyar APC, reshen jihar Rivers ta nemi hukumar zabe ta kasa INEC da ta dage ranakun gudanar da zabuka a jihar.

INEC ta ki amincewa ta karbi sunan yantakara daga jam’iyar kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyar har ta kai ga ya shafi zaben fidda gwanin da ta gudanar.

Akwai bangarori biyu a jam’iyar, daya karakashin jagorancin ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi daya kuma karkashin jagorancin sanata,Magnus Abe.

Tonye Princewill daraktan yada labarai da kuma tsare-tsare na dantakarar gwamna a tsagin Amaechi, Prince Tonye Cole shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa.

Ya ce bawa yan takarar APC karin wa’adin lokaci domin gudanar da yakin neman zabe abune da ya zama dole saboda tsaiko da aka samu sakamakon tirka-tirkar shari’a.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like