Jami’an tsaro sun yi awon gaba da tsohon shugaban hukumar tsaro ta DSS


Jami’an tsaro sun kama, Lawal Musa Daura tsohon shugaban hukumar tsaron farin kaya wato DSS.

An kama shine bayan da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya sauke shi daga kan muƙaminsa a yau da rana.

Osinbajo ya gayyaci Daura tare da babban sifetan ƴansanda na kasa, Ibrahim Idris, kan hana shiga majalisar tarayya da jami’an tsaron DSS suka yi.

An hana yan majalisun tarayya shiga harabar majalisar abin da ya janyo yada jita-jitar cewa gwamnati na shirin makarkashiyar tsige shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.

Manyan shugabannin hukumomin tsaron sun isa fadar Aso Rock a lokuta daban-daban.Yayin da Idris ya isa fadar da misalin ƙarfe 12:35, Daura ya isa da misalin karfe 1:15 na rana.

Bayan da ya yiwa mataimakin shugaban kasa jawabi, jami’an tsaro sun yi awon gaba da tsohon shugaban hukumar ta DSS.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like