Yan sanda sun rufe ginin sakatariyar jam’iyar APC dake Abuja.

Jami’an tsaron da suka yi wa ginin dirar mikiya sunce suna aiki ne da umarnin da aka basu daga sama inda suka kori dukkanin ma’aikatan da suke ciki.

Daga bisani an bawa wasu yan jaridu damar bisa sharudan cewa baza su yi tambayoyi ga ma’aikatan da suke cikin sakatariyar.

“Umarnin da aka bamu shine kada mu bari kowa ya shiga ciki amma muna aiki tare shi yasa muke anan wurin,”a cewar wani jami’in dan sanda dake wurin.