Jami’an tsaro sun kashe wani rikakken danfashi a Katsina


Rundunar ƴansandan jihar Katsina ta kashe wani rikakken dan fashi da makami mai suna Kane Muhammad wanda akafi sani da Ɗan-maikeke wanda yake cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sahannun jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan, SP Gambo Isa da aka kuma rabawa manema labarai a Katsina.

Isa ya ce an samu cigaban ne ranar 4 ga watan Janairu a yankin Old Market da yayi kaurin suna wajen tara batagari a karamar hukumar Bakori dake jihar lokacin da ƴansanda suke gudanar da sintiri.

Ya ce batagarin sun kai wa motar jami’an tsaron harin lokacin da suke sinitirin har ta kai sun raunata ɗansanda guda.

Jami’in hulda da jama’an ya ce ƴansanda sun harbe danfashin ne inda ya samu rauni daga bisani ya mutu a asibitin Bakori.

Ya kuma kara da cewa mutumin da ake zargi ya dade cikin jerin sunayen mutanen da rundunar take nema ruwa a jallo da suka addabi mutane a yankin Bakori da kuma Funtua.


Like it? Share with your friends!

-1
74 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like