Jami’an tsaro sun kama wani jigon jam’iyar PDP a Kaduna


Jami’an tsaro sun kama,Yaro Makama jigo a jam’iyar PDP ta jihar Kaduna.

Kamun nasa na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da aka kama,Ben Bako daraktan yada labaran yakin neman zaben jam’iyar PDP a Kaduna aka kuma tasa keyarsa a jirgin sama ya zuwa birnin tarayya Abuja.

An kama Bako ne saboda yin kalaman tayar da hankali cikin wani fefan bidiyo da aka dauka a lokacin da jam’iyyar ta ke gangamin yakin neman zabe a garin Kafanchan dake karamar hukumar Jama’a a makon da ya gabata.

Da yake magana kan lamarin mataimakin daraktan yakin neman zaben jam’iyar, Danjuma Sarki ya bayyana cewa wannan wani shiri ne na murkushe ƴaƴan jam’iyar gabanin zabe mai zuwa..


Like it? Share with your friends!

-1
77 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like