Jami’an sanda sun yi arangama da na Peace Corps a Abuja


Wasu jami’an ƴansanda da kuma na kungiyar sa kai ta Peace Corps sun yi arangama da safiyar yau a birnin tarayya Abuja.

Rikicin ya fara ne bayan da shugabannin kungiyar ta Peace Corps suka isa sakatariyar kungiyar ta kasa domin bikin cika shekaru 20 da kafa kungiyar a Najeriya.

Sama da shekara daya kenan da jami’an ƴansanda suka garkame sakatariyar uwar kungiyar dake Abuja.

Duk da umarnin da kotuna daban-daban suka bayar na buɗe sakatariyar rundunar yansanda ta yi kunnen uwar shegu da umarnin.

Shugabannin kungiyar sanye da bakaken kaya da aka rubuta ‘Muna kuka! Muna dana sani!’ ‘Muna alhinin doka da oda.’

Dickson Akoh, shugaban kungiyar na tsaka da yi musu jawabi lokacin da jami’an yan sanda suka shiga harba barkonon tsohuwa da kuma harba bindiga sama.

Mutane da dama ne suka jikkata a arangamar.

Ba wannan ne ba karo na farko da yan kungiyar ta Peace corps da kuma yan sandan suke arangama a bainar jama’a.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like