Jami’an Kwastan Na Ci Gaba Da Yin Dirar Mikiya A Wuraren Kasuwanci A Jihar Sokoto


A daidai ranar ta 1/10/2019, da Nijeriya ke murna da ranar samun ‘yancin kai, ranar da kuma mafi yawancin ‘yan Nijeriya ke murna tare da bukukwan cikar shekaru 59 na samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, a Sakkwato kam jami’an hukumar kwastan ne ke cigaba da dirar mikiya a shaguna da wuraren kasuwancin talakawa domin rufewa da kuma kwashe kayayyakin sana’ar tasu.

Jami’an hukumar ta kwastan din sun dira a wadansu wuraren sayar da motoci dake kan titin Maiduguri dake cikin garin na Sakkwato, inda suka kulle guraren, wadanda suka hada da, Jangwarzo Motors, Y, Ladan Motors, NA-IB Motors, Rahusa Motors da sauransu.


Like it? Share with your friends!

-2
99 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like