Jami’an Kwastam sun kama kunshi 1220 na ganyen tabar wiwi


Jami’an Hukumar Hana Fasa Kwauri Ta ƙasa, Wato kwastam dake aiki da shiyar Ikeja sun kama buhuna 39 da kuma wasu kunshi 1220 na ganyen tabar wiwi da aka boye cikin tsanaki a kasan buhunan tumatur da kuma wasu ganyayyaki.

Hukumar ta kwastam ta ce haramtaccen ganyen da darajarsu ta kai naira miliyan 10 anyi fasa kwaurin sune daga kasar jamhuriyyar Benin.

Kwantirolan shiyar, Muhammad Uba ya bayyana cewa ganyen da aka haramta shigo da shi an kama motar dake dauke da ita ne a yankin Olorunda dake jihar Ogun bayan da aka samu bayanan sirri dake nuni da cewa wasu gungun mutane na shirin shigo da ganyen tabar wiwi mai yawa zuwa Najeriya.


Like it? Share with your friends!

2
85 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like