Jami’an kwastam sun gano jarakunan man fetur 19 da aka boye a akwatin gawa


Hukumar hana fasa kauri ta kasa a ranar Laraba tace ta kama wasu jarkokin man fetur guda 13 masu cin lita 25 da kuma jarkoki 6 masu cin lita 10 da aka boye su cikin akwatunan gawa.

A wata sanarwa mai dauke da sahannun, Abdullahi Maiwada mai magana da yawun hukumar shiyar Ogun,ya ce an kama kayan ne a hannun wani mai fasa kauri lokacin da yake kokarin fita da su zuwa makotan kasashe cikin wata mota kirar Mazda lambar Legas.

Sanarwar ta cigaba da bayyana matsayar hukumar na bagudu baja da baya a yakin da take da masu fasa kauri.

Tun bayan da Najeriya ta rufe kan iyakarta da kasashen da take makotaka da su masu fasa kaurin ke sauya salo a kokarin da suke na cigaba da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Shi ma shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu da kaso 30 cikin dari tun bayan da aka rufe kan iyakokin.

Leave your vote

Comments are closed.

17 Comments

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg