Jami’an EFCC sun yi awon gaba da sirikin Atiku


Hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Taannati ta EFCC a ranar Asabar ta kama, Alhaji Babalele Abdullahi sirikin dantakarar shugaban kasa na jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Babalele wanda har ila yau shine daraktan harkokin kudi na rukunin kamfanonin Atiku an kama shi ne a gidansa dake Maitama.

Jami’an na EFCC sun shiga gidan cikin motoci biyu kirar Hilux da kuma Toyota Hiace.

Sun isa gidan da misalin karfe 08:30 na safe amma aka hana su shiga har sai da lauyansa yazo.

Bayan sun bincike gidan ba tare da samun wani abu na laifi ba daga nan sun wuce ya zuwa ofishinsa dake Oakland Center anan ma basu samu komai na laifi ba.

Daga bisani sun wuce da shi ofishin hukumar dake Maitama.


Like it? Share with your friends!

-1
69 shares, -1 points

Comments 3

Your email address will not be published.

You may also like