Jami’an EFCC sun kama wasu yan damfara 32 a Ogun


Jami’an hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati,EFCC sun sanar da kama wasu mutane 32 da ake zargi da aikata damfara ta Intanet.

Jami’an hukumar sun kama mutanen da ake kira yan “Yahoo-Yahoo Boys” ranar Alhamis a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

Shekarun mutanen da suka fada komar hukumar ta EFCC sun kama daga 15 zuwa 39 kuma ana kama sune rukunin gidaje na Liberty dake yankin Laderin a birnin na Abeokuta.

Kayan da aka samu a tare da su sun hada motoci masu tsada, kwamfitoci, wayoyin hannu da kuma takardun bogi.


Like it? Share with your friends!

-1
66 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like