Jami’ai sun ƙaryata barkewar cutar kwalara a gidan yarin Kontagora


Hukumar Dake Kula da Gidajen Yari, a jihar Niger ta ƙaryata labaran dake cewa an samu barkewar cutar kwalara da kuma tarin TB da ya jawo mutuwar ɗaurarru uku a jihar Niger.

Rabi’u Shu’aibu, mai magana da yawun hukumar ya ce rahoton karya ne.

“Babu barkewar cuta ko wace iri a gidan yarin Kontagora ko kuma sauran gidajen yarin mu dake jihar,” ya ce.

“Ɗaurarru biyun da suka mutu a gidan yarin sun mutu ne sakamakon kawo su da akai da matsalar ciwon hanta da kuma ciki.

“Duk da cewa jami’an kiwon lafiya na gidan yarin sun yi kokarin shawo kan lamarin lamarin nasu ya riga ya tabarbare kafin a kawo su gidan yarin.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like