Jam′iyyar FLN ta kama hanyar lashe zabe | Labarai | DWJam’iyyar FLN ta kasar Aljeriya ta lashe akasarin kujeru a zaben ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Hukumar zaben kasar ce ta sanar da hakan, sai dai duk da wannan nasarar, tana bukatar karin kuri’u kafin ta sami rinjaye a halin da ake ciki a kasar da ta sha fama da zanga-zangar neman sauyi.

Jam’iyyar ta FLN ta yi ma sauran fintinkau bayan da ta sami kujeru 105, Jam’iyyar Independent Candidates ta sami kujeru 78 a yayin da jam’iyyar MSP ta sami kujeru sittin da hudu. Ana bukatar kimanin samun kujeru 204 daga cikin 407 kafin jam’iyya ta sami rinjaye a majalisar kasar ta Aljeriya. Masana na ganin da wuya zaben ‘yan majalisar dokoki, ya yi tasirin kawo canji a dimukuradiyyar kasar.
 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg